Spinach rice

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

Sosai shinkafar nan tayi dadi abindai sai wanda y gwada dan da oga naci cewa yayi kamar ba shinkafa yake ciba.

Spinach rice

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Sosai shinkafar nan tayi dadi abindai sai wanda y gwada dan da oga naci cewa yayi kamar ba shinkafa yake ciba.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Alayyahu
  3. Mai
  4. Albasa
  5. Kwai
  6. Gishiri
  7. Bea leafs
  8. Cumine

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke tukunya ki zuba ruwa ki dora akan wuta inya tafasa ki debo shinkafa ki wanke ki zuba inta kusa dahuwa saiki tace a matsami.

  2. 2

    Saiki yayyanka alayyahu ki wanke da gishiri ki bare albasa ki wanke saiki yayyanka saiki dora tukunya kan wuta ki zuba mai inya fara zafi ki zuba albasa kiyita jujjuyawa harta dauko soyuwa saiki saka Bea leafs da cumine kiyita juyawa har albasar tayi laushi saiki juye alayyahun kiyita juyawa.

  3. 3

    Sai kiyita juya alayyahun har sai kinga alamar y fara laushi saiki fasa kwai ki kada ki zuba ki jujjuya harya hade jikin shi saiki juye shinkafar nan kiyita juyawa tsahon minti 5.

  4. 4

    In kika juya shinkafar tsahon minti 5 saiki rage wutar ki rufe ki barta ta turara tsahon minti 3 saiki sauke ki kwashe.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes