Umarnin dafa abinci
- 1
A wanke nama a gyara shi,idan da kitse a jiki a cire.A yanka shi iya girman da ake so naman ya kasance.
- 2
A zuba kayan kamshi da maggi akan kuli-kulin,a barbada maggi da kori da mai a jikin naman a juya sosai
- 3
Sai a dauki tsoka daya a saka a cikin kuli_kuli a juya sosai yanda zai nadi qulin sosai.
- 4
A shimfida foil paper a farantin gashi,sannan a jera naman akai,sai a saka a abun gashi a gasa naman sosai,ana yi ana dubawa har yayi laushi sosai.
- 5
A fereye dankali a wanke a yanka shi yadda ake bukata.A dora mai a wuta idan yayi zafi sai a zuba dankalin a wuta a soya
- 6
Suma su cucumber,karas,tattasai,albasa da tumatur a wanke su a gyara su
- 7
A zuba tsire a tsakiya a jera soyayyen dankali da karas,cucumber,tattasai da tumatur.
- 8
Aci dadi lfy😋🤤
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/13457262
















sharhai (3)