Alale da sauce

Girkin nan yayi dadi matuqa kuma naji dadinshi sosae
Alale da sauce
Girkin nan yayi dadi matuqa kuma naji dadinshi sosae
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke wakenki ki surfashi seki gyarashi ki wanke ki hada da attaruhu da albasa ki markada.Bayan kin markada seki buga shi na 'yan mintina.Daga nan seki xuba man gyada da manja (zaki iya amfani da mangyada in kinaso).Ki xuba maggi,onga,gishiri cikin tafasasshen ruwa ki jujjuya sannan ki xuba shi cikin kullin ki jujjuya seki kullasu a leda kiyi steaming dinshi har ya dahu.
- 2
In xaki hada sauce din naki xaki xuba mai ki soya albasarki ki kawo tafasasshen namanki ki xuba seasonings ki soya,ki xuba jajjagenki ki jujjuya kisa ruwa kadan ki rufe daga qarshe ki xuba yankakken carrot da cabbage ki rufe su turara shikenan kin kammala.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai