Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki yayyanka alayyahunki ki wanke sa sosai sai qasar dake jikinsa ta fita, sai ki saka a robarki mai fadi ki zuba sai ki kawo tafasasshin ruwan zafi ki zuba masa sai ki rufe sa sai yayi 30 minutes.
- 2
Sai ki hasa wuta ki dora tukunyarki akai ki kawo manja ki zuba sai ki dauko albasarki isassa da kika yanka ki zuba, daga nan sai ki dauko kayan miyanki da kika jajjaga ko kikayi greating sabida baa son ayi blending sabida baa son miyar tayi ruwa, sai ki dauko dafaffen namanki da kika riga kika tafasa, ki zuba ki jujjuya, sai ki saka kayan magginki, ki saka gishiri kadan, ki saka kayan qamshi ki jujjuya.
- 3
Sai ki dauko alayyahunki ki matse sa a gwagwa sai kin tabbatar babu ruwa a jikinsa sai ki zuba a cikin tukunyarki ki motsa sai komai ya hade jikinsa kamar minti 2 sai ki sauke. Shikenan miyarmu ta kammala 🤤
Similar Recipes
More Recipes



sharhai (3)