Sakwara da miyar alayyahu
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki bare doya ki Dora a wuta idan ya dahu ki daka a turmi idan yayi laushi ki mulmula ki kwashe a leda,ki wanke nama ki Dora a wuta ya dahu ki juye a roba
- 2
Sai ki soya manja ki zuba kayan Miyanki da dakanken tafarnuwa idan ya soyu ki zuba namanki da ruwan Naman ki juya
- 3
Sai ki kasa sinadarin dandanonki idan kayan miyar sun dafu kin dauko alayyahunki yankakke ki zuba karki bari ya dahu sosai
- 4
Shikenan miyar sakwara tayi ready to eat.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16296562




sharhai