Burabisko da miyar gyada

Yar Mama @YarMama
Kullum shinkafa hakan zai sa ta fita a rai, don Haka muke sarrafashi ta wasu hanyoyin ciki akwai biski da dambu.
Burabisko da miyar gyada
Kullum shinkafa hakan zai sa ta fita a rai, don Haka muke sarrafashi ta wasu hanyoyin ciki akwai biski da dambu.
Umarnin dafa abinci
- 1
Farko na gyara shinkafar sai na wanke tas
- 2
Na Shanya ya bushe
- 3
Sai na barza na tankade na Adana garin a gefe Zan yi kunu dashi wata rana in inada rai
- 4
Na daura ruwa a wuta nasa man gyada da gishiri. Sai na barshi ya tafasa
- 5
Na zuba tsakin shinkafar Ina ta juyawa har ya hade sai na rufe na rage wutan sosai na barshi ya turara.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16638449



sharhai (8)