Soyayyen dankalin turawa da kwai da red kabiji

Ummu haifa @08139604460F
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fere dankalinki ki wanke saiki yankasa a tsaye ki ajiye gefe.
- 2
Saiki dora Mai a wuta idan yayi zafi saiki dauko dankalinki ki saka gishiri kadan ki cakuda saiki saka a ruwan Mai ki soya, Amma karkibari ya soyu karau da laushinsa zaki barsa saiki kwashi ki ajiye gefe.
- 3
Zaki dauko kabejin ki kiyanka kanana ki yanka albasa ki kwankwatsa attarugu ki ajiye gefe.saiki zuba Mai kadan a pan saiki zuba albasa ki soya Sama-sama saiki dauko attarugu da cabeji kisaka saiki juya ki saka kayan dandano dana kamashi,
- 4
Saiki dauko dankalinki ki juye aciki saki motsa sosaiki saiki fasa kwai ki kada ki juye a ciki ki rufe ki rage wuta harya kafe jikin dankalin.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8268682



sharhai