Tuwon masara da miyar busasshiyar kubewa

#Sahurrecipecontest# tuwo na daya daga cikin,abincin gargajiya da nake so,shiyasa na yanke shawarar yi a lokacin *Sahur*
Tuwon masara da miyar busasshiyar kubewa
#Sahurrecipecontest# tuwo na daya daga cikin,abincin gargajiya da nake so,shiyasa na yanke shawarar yi a lokacin *Sahur*
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin miyar mu da tuwon
- 2
Da farko,za'a gyara kayan myar a jajja,hadi da daddawa da citta,sai a dora manja a wuta,a zuba su a soya,kamar na minti biyar,sai a sanya ruwan sanwa,a zuba gishiri kadan
- 3
Sannan a zuba magi mai dandano,a marmasa kifi,a cire kayar a zuba,sai a rufe rabin tukunyar,a barshi ya nuna na tsahon minti arba'in da biyar
- 4
Gashi bayan ya nuna,sai arika zuba kubewar ahankali,ana kadawa,har yayi kauri kadan,ba dayawa ba,sai a kuma bari yayi kamar minti goma,a janye wutar,sannan a sauke.
- 5
Ga miyar busasshiyar kubewar mu ta hadu.Aci lafiya.
- 6
Tuwon masara.Garin masara,ungurnu,ruwa...Dafarko za'a zuba ruwan ungurgun kadan a kan garin,sai a bi da ruwa,a jujjuya,su hade,adama da dan kauri kadan.
- 7
Sai dora ruwa a wuta ya tasafa,sannan a zuba ayi talge,abarshi ya nuna,na tsahon minti talatin,sannan a tuka tuwon,kada acika gari,sai a rufe ya silala kamar na mitin biyar,sannan a sauke a kwashe aci da miyar kubewar.
- 8
Ga sakama ko,Aci lafiya
Similar Recipes
More Recipes






















sharhai