Stuffed yam cake
Kitchenhuntchallenge
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko dai zaki fere doyar ki,kisaka ta a tukunya kisa ruwa da gishiri ki bari ta dahu sosai
- 2
Sai ki dafa nama,kiyi blending ko ki daka a turmi
- 3
Sai ki soya naman kisa citta da tafarnuwa da kayan dandano da na kamshi
- 4
Sai ki dauko doyar da kika Dafa ki daka ta a turmi ko kuma kisa cibi me yatsu ki dame ta har ta zama gari,sai ki fasa kwai 1 ki zuba a cikin doyar
- 5
Ki dauko garin biredi ki zuba a cikin doyar,ki motsa su sosai har su hade
- 6
Sai ki rika diban doyar kina mulmula ta sai ki buda tsakiyan ta ki saka naman da kika soya a ciki,sai ki sake mulmulata don ki rufe naman da ke ciki
- 7
Sai ki saka a tafin hannun ki kidan matsa shi Kadan ya danyi flat,sai ki soya a cikin ruwan mai
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9380159




sharhai