Ilokar Madarar gari mai kwakwa

Salwise's Kitchen @cook_16516066
Ilokar madarar gari nada dad'i da gard'i ..
Ilokar Madarar gari mai kwakwa
Ilokar madarar gari nada dad'i da gard'i ..
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin mu kamar haka.Da farko za'a dora ruwan da sikari a wuta,a barsu s dafu,idan ya dan fara danko
- 2
Sai a cukuda gurzajjiyar kwakwa da garin madara
- 3
Sai azuba cikin sikarin akan wutan
- 4
Ayita tukawa da muciya,ana dan zuba mangyada kadan
- 5
Har sai yayi kalar ruwan kasa (golden brown)
- 6
Sannan ashafa mangyada a leda ko a zuba a roba,ajuye
- 7
Sai a sanya cokali arika diba ana sakawa a faranti har agama,abarshi ya sha iska..sai asha.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9528382





sharhai