Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki sami robar ki me kyau saiki zuba fulawar ki aciki sai kisa attaruhu da albasar ki da kika jajaga su, kizuba aciki saiki zuba maggi da gishiri saiki dauko ruwanki ki zuba aciki dai dai yanda bazaiyi ruwa ba ki kwaba da ludayin ki me kyau harsaita kwabo, amma karki bar tayi ruwa bayan kin gama saiki ajje a gefe. Ki dauko kasko ki me kyau ki daura akan wuta saiki zuba manja kadan ki dinga debo wannan fulawar da kika kwaba da ludayin ki kina zubawa acikin kaskon ki saiki barta ta soyo
- 2
Idan ta soyo saiki juya bayan ta idan ta soyo sai ki sa a flate. 😋
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9564985








sharhai