Miyan taushe

Fatima Ibrahim (Albint, s cuisine)
Fatima Ibrahim (Albint, s cuisine) @cook_16558221
Bauchi

Wannan miya ba a bawa Mai kiwuya, tayi dadi sosai

Miyan taushe

Wannan miya ba a bawa Mai kiwuya, tayi dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti 45mintuna
5 yawan abinchi
  1. Alaiyaho
  2. Yakuwa kadan
  3. Jajjagen kayan miya
  4. Maggi dunkule
  5. Manja
  6. Man gyada
  7. Dakakken gyada
  8. Nama tafashe
  9. Ruwan nama

Umarnin dafa abinci

Minti 45mintuna
  1. 1

    Da farko na daura man gyada na a wuta sai na zuba kayan miya na bar shi ya soyu sai na zuba ruwan nama da dunkulen maggi, da sauran kayan qanshi sai na rufe na bar shi ya tafasa sai na zuba dakakken gyada na bar shi ya nuna kaman minti 30

  2. 2

    Na gyara alaiyaho na yanka shi,na gyara yakuwa na ma na yanka, na wanke su a ruwan gishiri na tsane a mararaki (colander) na ajiye a gefe. Sai na koma kan miya na dake wuta na zuba manja da nama na motsa ta sai na zuba ganyen alaiyaho da yakuwa na rufe tukunyan na bar shi ya turaro, sai na motsa shi,da ganyen ta nuna sai na sauqe naci da tuwon shikafa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima Ibrahim (Albint, s cuisine)
rannar
Bauchi
Cooking is my hubby , which I can't do without
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes