Farfesun kayan ciki

A duk lokacin da nake son shan farfesu, na kan je ga farfesun kayan ciki domin baya kawo wata illa a jiki sannan gashi ina jin dadin sa.
Farfesun kayan ciki
A duk lokacin da nake son shan farfesu, na kan je ga farfesun kayan ciki domin baya kawo wata illa a jiki sannan gashi ina jin dadin sa.
Umarnin dafa abinci
- 1
Tanadi kayan da ake bukata
- 2
Wanke kayan ciki, zuba a tukunya mai tsabta, sa ruwa masu dama yanda kike bukata ki dora a wuta sannan ki zuba duka kayan hadi banda attaruhu da tattasai
- 3
Barshi yayi ta dahuwa har sai ya fara laushi sannan ki zuba nikakken attaruhu da tattasai aciki, ki rufe ki barshi ya cigaba da dafuwa har sai yayi laushi
- 4
Bana saka oil a pepper soup ko wane iri zanyi saboda yafi mani dadi a haka sannan naman yana da maiko a jiki wani lokaci.
- 5
Shi kenan farfesun kayan ciki ya hadu, za'a iya ci hakanan ko da bread, gurasa, shinkafa da sauransu.
Similar Recipes
More Recipes






sharhai