Yadda zaki hada fondant
Yadda zaki kware wajan fondant
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki hada kayan yin ki kamar haka
- 2
Sai ki sami kwano dan karami sai ki zuba gelatine ki kamar cokali biyu ki sa ruwa kamar cokali 4 haka ki juya
- 3
Sai ki juya shi amma zaki ka yayi miki dan burtsatsai beyi smooth ba,to mafita a nan zaki zuba ruwa a tukunya ki dora akan wuta amma ruwan ba me Yawa ba yadda idan kin sa kwanon da kika zuba gelatine din bazai sha kan sa ba sabida shi gelatine ba,a dora shi direct kan wuta sai dai a sa shi cikin ruwan zafi ana juyawa har ya narke ya koma ruwa ruwa(syrup)
- 4
Sai ki sa glucose yadda na fada miki ki,ki juya sosai sanna sai ki sauke,sai ki zuba flavour, corn syrup, glycerine ki juya sanna ki dan sa pinch na salt da butter zaki ga kamar haka a hoton
- 5
Sai ki kawo icing sugar ki fara zuba kamar 2cup tare da cmc dama nafada miki yadda zaki sa shi sai ki juya
- 6
Sai kina karawa kina juyawa kamar kina kwabin dough a haka zaki ga yana kwari har sai kinga ya daina kama miki hannu
- 7
Sanna idan kina yi ki tabbara kina yishi a kan laida ko irin waje me kyau da tsafta kuma idan kina murzawa kada kina yi da yatsu tafin hannu zaki sa kamar yadda zaku gani
- 8
Idan yana kamawa zaki iya barbada corn flour a kasan wajan ko icing sugar zaki ga idan yayi sosai zai dena kama miki hannu zai zama dough sosai sai ki sami Leda ki sa aciki yadda iska bazata shiga ba ya daskare
- 9
Sai kiyi kwalliyar da kike so idan wani kala kike so zaki iya sawa ki murza shi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai