Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki tafasa ruwan zafi sai ki zuba akan shinkafanki na tsawon minti 15.
- 2
Ki samu tukunya kisa manja ki yanka albasa ki soya su
- 3
Ki sake yin jajagen attarugu da albasan da garlic da danyen cittan ki sai ki zuba akan manjan
- 4
Ki matsa tumatir din Leda rabi akai ki gauraya ki soyasu tare
- 5
Ki tsaida ruwa daidai yadda zai isa ya dafa miki shinkafan
- 6
Ki wanke kifin ki ki zuba aciki,kisa da signature jallof dinki
- 7
Ki sa dandano ki rufe ki barshi ya tafasa,in kifin yadanyi laushi sai ki zuba wankeken shinkafan ki aciki ki rage wuta.
- 8
In ya kusa tasnewa sai ki wanke yakuwan ki ki zuba ki rufe ki barshi ya tsane kafin ji juya yakuwan.
- 9
In yayi sai a sauke.
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/9860186




sharhai