Couscous da sause in kabeji
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki zuba mai kadan a pan inki sae ki zuba couscous inki sae ki juyashi har sae jikinshi y hade da mai sae ki juyeshi a roba me kyau
- 2
Sae ki wanke koren tattsai ki yayyankashi ki zuba acikin couscous sae ki motse
- 3
Sae ki yayyanka karas inki ki wankeshi ki zubashi atukunya ya dahu dae dae yanda kikeso sae ki tsaneahi a gwagwa
- 4
Sae ki zubama couscous inki ruwa(Rabin kofi) a leda daya na couscous(acikin ruwan zaki saka curry) sae ki kawo karas inki ki hadesu ki juya,sae ki rufe zuwa minti biyar,,,,,ya sauka
- 5
Sae ki dauko wankakken tukunya ki zuba Mai, tarugu da Albasa sae sun dan fara soyuwa
- 6
Sae ki yayyanka kabejinki da karas ki wankesu ki tsanesu cikin gwa-gwa idan y bar zubar ruwa sae ki kawoshi ki zuba cikin suyarki,ki zuba dandano,ki saka kayan kamshi sae ki motse ki dan rufeshi zuwa mint 5 sae ki bude ki motsa,sause inki ta kammala
- 7
Ya sauka 🤗
Keywords
Similar Recipes
More Recipes







sharhai (2)