Kwantalakan alabo da fulawa

Kwantalakan alabo da fulawa
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko kisamu roba Mai kyau,sai kizuba flour,garin alabo,da gishiri kadan ki gawraya sosai su hade.
- 2
Sanna ki dauko ruwa kina zubawa bit by bit har sai ya hade yazama dough Amma kada yayi tauri Kuma Kar yayi ruwa ruwa.Kamar de Haka👇.
- 3
Sannan ki samu tray ki bar bada flour akai saboda kada ya manne a jikin tray din, like dis.👇
- 4
Sai Kuma kudunga gutsira kadan kina mulmulawa Kamar de Haka 👇.Yawwa
- 5
Sannan ki ajiye akan tray din,Haka zakici gaba dayi kina bada flour akai saboda gudun hadewa.😊
- 6
Kamar de wannan danayi👇💕
- 7
Sannan a daura ruwa akan wuta kibar shi Yar ya tafasa😉.
- 8
Sannan ki zuba kwantalakan ki a hankali har ki juye dukka, sannan ki juya a hankali sbd gudun hadewa wake guda. Kamar yadda nayi.
- 9
Kibarshi ya tasa har na tsawon minti 15.
- 10
- 11
Sai ki samu roba kisa ruwa,ki tsame shi acikin ruwa Mai kyau sanna ki Kara tsamewa zuwa mazubin da zaki hada ki tabbata Babu ruwa aciki.
- 12
Haddeden kwantalakan alabo ku ya kammala.
Ina matukar son nacishi da manja sannan na zuba Masa sauce din albasa akai.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





















sharhai