Awara da kwai

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti talatin
mutum uku
  1. Waken suya Kofi biyu
  2. Lemon tsami guda hudu
  3. Kwai uku
  4. Kayan dandano
  5. Albasa 1
  6. attarugu 5

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    A debi waken suya a tsinke tsakuwar, a wanke da ruwa dattin ya fita tas.

  2. 2

    A jika shi Kamar na mintuna talatin idan a blender za a markada, idan Kuma a inji ne to ana wankewa za a iya kaiwa a markada. Bayan an markada a qara ruwa a kullin a rinqa zubawa a abun Tata ana matsewa har sai an cire madarar.

  3. 3

    A juye madarar a tukunya a daura akan wuta ta tafaso, yayin da take tafasa a zauna kusa inba haka ba zata zube, a saka gishiri da ajino cikin ruwan in ana buqata harda atargu da albasa.

  4. 4

    A matse ruwar lemun tsami a roba a tace sabida kwallayen su fita.

  5. 5

    Yayin da awara ya tafaso sai a zuba ruwan lemun tsami a ciki, zamuga ta fara dunkulewa,

  6. 6

    Mu lura, zamuga saman ya zama Madara a chure kasan Kuma ruwa, ba lalle sai ya hade wuri daya ba,

  7. 7

    Idan mukaga ruwa irin normal ruwa haka ciki to ya dahu.

  8. 8

    Sai mu nemi abun Tata ko Kuma matsantsami mu juye a ciki mu barshi ya tsiyaye ruwan jikinshi Amma ba dika ba. Da zaran ya hade jikinshi shikenan. Mu yanka irin shape din da mukeso

  9. 9

    Mu fasa kwai mu zuba albasa da atarugu ciki da Maggi mu rinqa jefa awarar ciki muna soyata a Mai.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
HAFSAT ABDULKAREEM
rannar
A food lover.❤️always ready to learn something new in zha kitchen 🍽️🍩😍
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes