Umarnin dafa abinci
- 1
Dar farko zaki samu kifi ki wanke da ruwan kal, ko lemun tsami
- 2
Idan kin gama wankewa ki samu gishiri da maggi ki zoba dan dai dai sai ki barshi ya kafe tas babu ruwa a cikin sa
- 3
Sai ki samu mangyada dan dai dai, tafarnuwa, citta, curry, thyme ki hada guri daya.. ki dauko kifi ki shafe a jikin sa
- 4
Kiyi pre- heating oven na minti 20 sai ki dauko kifi ki jera a bakin tray ki saka sa a oven ki gasa sa a 150 Degree
- 5
Sai ki samu fry pan ki zoba dan mai, albasa, tafarnuwa,citta ki soya idan ya zama golden brown sai ko ruba tarugu, koren tattasai, jan tatsai carrot
- 6
Ki Dan basu tsoro a wuta ki saka abun dandano dan kadan saboda ki gasa kifin da kayan dandano
- 7
Sai ki Ciro kifin ki saka a cikin sauce din da kika hada ki juya a hankali
- 8
Idan sauce din ya bi jikin kifin sai ki saka a plate
- 9
Zaki iya ci don marmari, ko da farar shinkafa, farar taliya da sauran su
- 10
Zaki iya decorating da lemon tsami, dankalin turawa da kabeji
- 11
Aci lfy😁😁
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai