Awara me sauce

Wakan suya yana da amfani sosai a jikin dan adam.
Ina matukar son awara tana da dadi sosai
Awara me sauce
Wakan suya yana da amfani sosai a jikin dan adam.
Ina matukar son awara tana da dadi sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki tinci soya Bean's dinki, seki wanke shi ki Kai a markada Miki,
- 2
Idan aka dawo daga nika saiki taceta da abin tadar koko saiki hura wuta ki dora tunkaya ki zuba wakin soyar da aka markada miki kirufe
- 3
Idan ta tasaso dama akwai Dan tsamin/ tsamiya / alimin a gefe seki dinga zubawa akalla tana tafasa uku kafin ta dahu,
- 4
Idan ta dahu,zakiga da kanta tana dunkule wa seki dauko abin tatar koko ki tace ki kan dara mata wani abu me nauyi akanta tadan hade jikinta sosai
- 5
Seki yanka ta yanda kike so ki dora Mai a kasko ki soya awararki Sama Sama sai ki tsameta
- 6
Ki dan zuba mai akasko kadan dama kin jajjaga attaruhu kin yanka albasarki sai ki zuba su a kaskonki ki dan basu tsoro sai ki zuba Maggi da dan kayan kanshi kadan sai ki juya
- 7
Daga nan sai ki zuba awararki ki juyata a ciki kayan hadin su Shiga jikanta shikenan kin gama sai ci😋😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes







sharhai (2)