Yam balls da sauce
Yam balls abinci ne wanda akeyin sa da doya,yana da matukar dadi ba kadan ba. Zaa iyacin sa a matsayin karin kumallo da safe a hada da shayi.. zaa iya cinsa da lemo me sanyi. Zaa iyayi wa yara su tafi dashi makaranta #yamrecipecontest

Umarnin dafa abinci
- 1
A samu doya a ferayeta a wanke a zuba a tukunya da ruwa a dafata ta dahu a sauke a tace ruwan a barta ta huce
- 2
Bayan doyar ta huce a murmushe ta
- 3
A dauko ni'ka'kken nama da markadandan attaruhu da albasa a zuba a cikin murmusashiyar doyar a juya
- 4
A zuba sinadarin dandano da gishiri da kayan 'kanshi da curry a cikin hadin mu na doya
- 5
A cuccura hadinmu na doya izuwa dun'kule-dun'kule
- 6
A samu kwai a fasa a cikin mazubi me kyau a dan marmasa sinadarin dandano
- 7
A dora mai a huta in yayi zafi a dauko kwai ana tsoma curarriyar doyar a cikin kwan ana sawa a cikin mai har sai ya soyu sai a kwashe a faranti
- 8
Sai sauce din mu zaa wanke albasa tumatir, attaruhu da karas a cikin ruwa me kyau da gishiri
- 9
A yanyanka su a dora a kan wuta a zuba ruwa kadan da sinadarin dandano da kayan kamshi har sai ya dahu sai a sauke
- 10
Sai a dauko yam balls a jera a faranti a zuba sauce a gefe 😋😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai