Gasashshen meat pie

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Gasashshen meat pie, kasancewar anfi yin soyayye yasa na kawo muku yanda akeyin gasashshe. Yanada mutukar dadi sosai.

Gasashshen meat pie

Gasashshen meat pie, kasancewar anfi yin soyayye yasa na kawo muku yanda akeyin gasashshe. Yanada mutukar dadi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 30mintuna
Guda 9 manya
  1. 2Fulawa Kofi
  2. Bakar hoda 1/2 cakali
  3. Butter cokali 3
  4. Kayan kamshi kadan
  5. Curry kadan
  6. 2Magi guda
  7. Dankalin turawa guda 2 manya
  8. Nama yanka 5 madaidaita
  9. Parsley cokali 2 yankakke
  10. cokaliAttaruhu jajjagagge Rabin karamin
  11. 4Gogaggiyar albasa cokaki
  12. 1Kwai guda
  13. Ridi cokali 2
  14. Mai
  15. Butter cokali 1 don't shafawa a farantin gashi
  16. m

Umarnin dafa abinci

minti 30mintuna
  1. 1

    A zuba mai a kasko Idan ya dau zafi sai a zuba albasa, a juya a zuba ruwa cokali 1, a motsa minti 2 sai a zuba attaruhun a motsa, a zuba naman shima a motsa na minti 3 sai a juye dankalin a ciki a saka magi, curry parsley da spices a juya a bashshi ya karasa sai a sauke.

  2. 2

    A tankade fulawa a zuba butter, magie guda 2, bakar gode, gishiri kadan da spices a juya sai sun hade guru daya sannan a zuba ruwan dumi a kwaba. Har sai ya hade jikinsa

  3. 3

    A yayyanka kwabin, sannan a barbada fulawa a abin murji a dunga fadadawa sai a saka a abin dannewa a shafa ruwa a bakin sannan a zuba hadin a danne.

  4. 4

    A shimfida foil paper a kan farantin gashi sai a shafa butter sai a dunga jera meat pie din akai

  5. 5

    A kada kwai sannan a yi amfani da brush na kitchen a shafa a saman meat pie din.

  6. 6

    A kawo ridi a barbada a saman meat pie din.

  7. 7

    A kunna oven a barshi yayi zafi sai a rage wutar a saka tray din a ciki a barshi ya gasu sai an ga ya fara zama ruwan Zuma sai a cire.

  8. 8

    A juye a kwano. An gama

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes