Panke (puff puff)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Abuja

Wato Ina matukar son panke Amma jefawa na bani wuya. Ni kuma nasa naci akan sai na koya wasa wasa inata trying na cup daya zuwa biyu Amma gashi ayau na zama gwana wajen yin panke

Panke (puff puff)

Wato Ina matukar son panke Amma jefawa na bani wuya. Ni kuma nasa naci akan sai na koya wasa wasa inata trying na cup daya zuwa biyu Amma gashi ayau na zama gwana wajen yin panke

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya
Uku
  1. Fulawa cup biyu
  2. 1/3 cupSugar
  3. Yeast chokali daya
  4. Dan gishiri
  5. Dan flavor idan da bukata
  6. Madara chokali daya
  7. Ruwa 1 & 1/4cup
  8. Sai mai na soyawa

Umarnin dafa abinci

Awa daya
  1. 1

    Da farko zaki samu babban kwano ki rankade flour ki

  2. 2

    Sai ki zuba suga, yeast, dan gishiri, madara, kawai dai ki zuba duk ingredients dinki banda mai dan shi za a soya panken ne dashi

  3. 3

    Sai ki kwaba da ruwan dumi ki ajiye a guru mai dumi dan ya tashi

  4. 4

    Daga nan sai kisa mai a wuta ki fara soyawa kina juya was dan kalan su zama iri daya

  5. 5

    Gashinan ya fara soyuwa

  6. 6

    Shikenan sai ka kashe idan ya miki kalan da kikeso

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
rannar
Abuja
cooking is my dream and also cooking is all about being creative
Kara karantawa

Similar Recipes