Donut

Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
Sokoto

Donut Dina ya yi laushi da dadi ya kuma tashi sosai.

Donut

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Donut Dina ya yi laushi da dadi ya kuma tashi sosai.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

dunut 16 yawan abinchi
  1. 4Fulawa Kofi
  2. Butter kwatan Leda
  3. Suga kwatan kofi
  4. Gishiri kadan
  5. Yeast babban cokali 1
  6. 1Madara Kofi
  7. 1Kwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za ki tankade fulawarki a mazubi me kyau ki ajiye a gefe, se ki hada madara, butter, sugar, yeast,kwai da gishiri a wani mazubin ki motsa sosai, ki bar hadin na minti biyar sannan ki zuba fulawa a hankali kina juyawa har su hade jikinsu.

  2. 2

    Ki mayar da kwabinki a wuri me tsafta ki barbada fulawa ki ci gaba da murzawa na tsawon minti biyar, ki rufe kwabinki ki ajiye a wuri me zafi na tsawon awa daya. Bayan awa daya kwabin ya tashi ya lunka yanda ya ke,

  3. 3

    Ki dauko fulawarki ki fara murzawa ta yi Fadi kada ta yi kware da tudu, se ki sake barinta na tsawon minti biyar kafin ki yanka donut dinki. Ki yi amfani da cokali mai Fadi ki dauko donut dinki da Shi, yin amfani da hannu ze sa ya canza siffa se ki soya.

  4. 4

    Ki juya daya gefen idan gaban ya yi, ki kwashe idan ko ina ya soyu. A ci dadi lfy.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
rannar
Sokoto

sharhai

Similar Recipes