Donut

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Ina son donut gaskia gashi yayi dadi sosai musan man idan aka hada shi da wani abu mai sanyi kamar zobo da sauran su

Donut

Masu dafa abinci 6 suna shirin yin wannan

Ina son donut gaskia gashi yayi dadi sosai musan man idan aka hada shi da wani abu mai sanyi kamar zobo da sauran su

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi hudu
  2. Suger kofi daya
  3. Kwai daya
  4. Yeast cokali biyu da rabi
  5. Butter cokali biyu
  6. Cokalin shan shayi na flavour
  7. Madara cokali biyu ba dole ba
  8. Mai kofi ukku wanda zaa soya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki tankade fulawar ki sai ki zuba ta a roba ki zuba sauran kayan hadi baki daya ki motsa su sanan ki samu ruwan mai dumi ki kwaba kamar kofi daya haka zaki zuba kina zuwa a hankali kina kwabawa

  2. 2

    Har sai yayi kamar dai yana dan kama maki hannu kada kiyi shi da ruwan sanan sai ki dauke shi ki dinga bugawa kina saka yar fulawa a hannu ki dan kada ya kama maki hannu kiyi kamar minti 30 kina bugawa idan ya bugu sosai zaki ga kwabin ki yayi kyau sosai

  3. 3

    Bayan nan sai mulmula shi kamar kwallo kana kana ba manya ba ba kuma kana sosai ba sai ki barbada fulawa akan tire ki dinga jerawa

  4. 4

    Bayan kin gama sai ki kai shi a rana ki bashi kamar minti 30 haka zai Tashi zakiga yayi girma yayi ukkun wanda kikayi inde yeast din nada kyau

  5. 5

    Bayan nan sai ki dauko Shi kisa dan yatsan ki na tsakiya kiyi masa huda zaiyi kamar donut din sai ki sa mai yayi zafi amma kada ki bari yayi zafi da yawa sai ki rage wutar ki dinga saka donut din kina soyawa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

sharhai

Similar Recipes