Danderun naman rago

karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
Kano

Wannan danderu na naman rago wani sabon salo ne da nabi don sarrafa naman sallata don jin dadin iyalina da kuma baki da suketa kawo min ziyara na sallah. Na kasance ako da yaushe inason naga sabon samfuri na yanda zan yi abu don a ci a yaba. A baya ina yawan yin danderu irin wannan amma na kaza kawai nakeyi.wannan karon nace bari na gwada yin na naman rago kuma masha Allah babu wani bambanci wajen sarrafawar da kuma dahuwar. Yana da kyau kwarai mu dage don ganin mun canza sanwa ta hanyoyi daban daban don jin dadin iyalan mu da kuma abokan arziki. Ina fata zaa gwada wannan recipe din don a ji abinda nima naji.#NAMANSALLAH

Danderun naman rago

Wannan danderu na naman rago wani sabon salo ne da nabi don sarrafa naman sallata don jin dadin iyalina da kuma baki da suketa kawo min ziyara na sallah. Na kasance ako da yaushe inason naga sabon samfuri na yanda zan yi abu don a ci a yaba. A baya ina yawan yin danderu irin wannan amma na kaza kawai nakeyi.wannan karon nace bari na gwada yin na naman rago kuma masha Allah babu wani bambanci wajen sarrafawar da kuma dahuwar. Yana da kyau kwarai mu dage don ganin mun canza sanwa ta hanyoyi daban daban don jin dadin iyalan mu da kuma abokan arziki. Ina fata zaa gwada wannan recipe din don a ji abinda nima naji.#NAMANSALLAH

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

2hrs
2-3 servings
  1. Naman rago rabin kilo
  2. Tarugu manya guda goma
  3. Albasa manya biyu
  4. Carrot madaidaita guda shida
  5. Danyen citta madaidaici
  6. 6 Tafarnuwadanye guda
  7. Ganyen naa naa cokali babba daya
  8. Maggi guda bakwai
  9. Gishiri karamin cokali daya
  10. Yoghurt babban cokali hudu
  11. Lemon tsami babba guda daya
  12. Mangyada babban cokali hudu
  13. Foil paper
  14. Curry karamin cokali daya
  15. Thyme karamin cokali daya
  16. Turmeric karamin cokali daya
  17. Red chilli powder teaspoon
  18. Ground sage teaspoon daya
  19. Seasoned meat tenderizer, teaspoon daya
  20. Dry oregano teaspoon daya
  21. Ground white pepper teaspoon daya

Cooking Instructions

2hrs
  1. 1

    Ga hoton kayan da nayi amfani dasu wato ingredients din da kuma hotunan spices dana lissafo sunayensu kowanne don a fahimta.

  2. 2

    Da farko zaa juye naman ragon da aka riga aka wanke shi tas a ka tsane ruwan jikinshi duka. Zaa zuba naman a kwano babba ko roba mai zurfi.

  3. 3

    Zaa jajjaga tarugu daban albasa ma daban tun kafin a zo hada naman. Sai a zuba su akan naman bayan an juye a cikin kwano.

  4. 4

    Sai a zuba mangyada akai asa cokali babba na diban miya ko wooden spoon a jujjuyasu sosai.

  5. 5

    Sai a zuba yoghurt din akai

  6. 6

    Anan zaa zuba gishiri,maggi,naa naa da aka yanka kanana sosai,curry thyme,turmeric, white pepper, sage,chilli powder da dry oregano.sai a raba lemon tsamin gida biyu a cire kananan kwallon da ke tsakiya a matse ruwan akan naman. A sami grater karama a yi grating citta da tafarnuwa a saman naman sai a yita juyawa da babban cokalin har tsawon mintuna uku sai a rufe shi a sa a fridge yayi kaman mintuna talatin zuwa awa guda.

  7. 7

    Zaa sami baking tray, wato trayna gashi wanda ake sawa a cikin oven a shimfida foil paper a kai.

  8. 8

    Sai ki juye hadin naman ragon akai.

  9. 9

    A wajen hada naman munyi grating albasa daya sauran dayan kuma an yanka ta manya manya. Sai a zuba albasar akan naman.

  10. 10

    Nan kuma carrot da aka yanka dogo dogo(Julienne) zaa zuba bayan an zuba albasar.

  11. 11

    Sai ki nannade foil din a hankali ki rufe koina sosai yanda iska ba zai samu shiga ba.

  12. 12

    Nan oven ne dama na kunna shi yayi mintuna talatin. Zaa maida wutar ta koma low heat sai a dora karamin tray din akan babban can sama ba kusa da wutar sosai ba yanda zai gasu a hankali. Na gasa shi tsawon awa guda sannan na fiddo shi na jujjuya na maida cikin oven din ya kara yin mintuna talatin sai na cire na kashe wutar.

  13. 13

    Shi wannan danderu yana da dadi matuka kuma zaa iya bin wannan hanyar wajen yin danderun kaza,kayan ciki,kifi ko ma naman saniya. Zaa iya cin sa da farar shinkafa,fried rice, Chinese rice,doya,taliya,couscous ko makaroni.

  14. 14

    A gwada a ci dadi lafiya!

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
on
Kano

Similar Recipes