Rubaben taliya da yakuwa

HALIMA MU'AZU aka Ummeetah @cook_12470582
Wannan abinci ne me sauki baya bukatar soye soye, be daukan lokaci kuma ga dadi
Rubaben taliya da yakuwa
Wannan abinci ne me sauki baya bukatar soye soye, be daukan lokaci kuma ga dadi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da fari zaki zuba ruwa a tukunya, ki sa manja, ki wanke yakuwa ki zuba
- 2
Ki jajjaga tarugu, albasa 1 da tattasai ki zuba, kisa gishiri da dandano
- 3
In ruwan ya tafasa sai ki karya taliyar ki zuba, ki motsa dan kar ta hade, sai ki rufe tukunya ki bari ta bararrako
- 4
Sai ki yanka ragowar 1 albasan in taliyar ta dauko nuna sai ki zuba, ki rufe na minti 2 sai ki sauke
- 5
Ayita da dan ruwa ruwa kuma aci da zafinsa.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11053917



sharhai