Taliyar zogala
#taliya tana cikin abinchi dakeda saukin dafawa akoda yaushi wannan dahuwar de, saka mata zogala a ciki ya kara mata inganchi wurin gina jiki.
Taliyar zogala
#taliya tana cikin abinchi dakeda saukin dafawa akoda yaushi wannan dahuwar de, saka mata zogala a ciki ya kara mata inganchi wurin gina jiki.
Umarnin dafa abinci
- 1
Sinadiran hada wannan taliyar ta zogale
- 2
Zaki dauko manki ki zuba cikin tukunya idan yayi zafi seki dauko tarugu tattasai da albasa ki zuba. Kinayi kina juyawa har ya soyu.
- 3
Cikin wata tukunya daban ki zuba nikakkun kayan miya ki soya ya soyu idan sun soyu seki dauko su ki juye cikin dayar tukunyar ki motse su
- 4
Se kidauko magi, farin maggi, curry,kayan kanshi se kizuba cikin suyarki kamar yadda kika gani a hoto ki soyasu tare su soyu
- 5
Sai ki dauko ruwanki ki zuba yawan yadda kike so,(wasu nasonta da ruwa wasu nasonta tsane) ki zuba lawashinki da zogala ki rufe tukunya na dan tsawon lokachi
- 6
Se kidauko taliyarki ki karyata kizuba ciki. ki motsa dan kada ta damke wuri daya se ki dauko marfi ki rufe
- 7
Idan ta kusan tsanewa se ki zuba alayyahun ki da albasa ki rufe ta gama sulala
- 8
Shike nan yaliyarki ta gama haduwa se ci hmm ba aba yaro me Kyuya😀
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





















sharhai