Dafadikan shinkafa da kifi da salaq

Ummu Fa'az @Ummfaazs_kitchen
Dafadikan shinkafa da kifi da salaq
Umarnin dafa abinci
- 1
A dafa ruwa inyayi zafi a xuba shinkafa abari ya tafasa inyayi tafasa daya biyu se a sauke a wanke shinkafar tas.
- 2
A jajjaga tumatir, tattasai, attarugu, tafarnuwa da albasa.
- 3
A wanke kifi a dafa ta da kayan dandano asa ruwan dahuwar a gefe a soya kifin.
- 4
Mai sa man da akasoya kifin a tukunya daidai Wanda ze Isa yin dafadikar.
- 5
A ynka albasa a ciki a xuba jajjagen asa curry, Maggi, gishiri abari ya soyu.
- 6
Inya soyu se a sa ruwan kifin a Kara wani ruwan kadan. Asa kayan dandano da onga abari ya tafasa.
- 7
Inya tafasa se a xuba shinkafar a Bari ya dahu.
- 8
A wanke lettuce sosai a yanka asa a gefe, se a wanke cucumber a sa gefe shima da tumatir da albasa.
- 9
A ci lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11771337



sharhai