Jollof din taliya da macaroni

farhas_cuisine @cook_21003425
Jollof din taliya da macaroni
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki tafasa naman ki da albasa, maggi da gishiri dan kadan da kayan kamshi
- 2
Sai ki zuba mai kadan a tukunya idan yayi zafi sai kisa naman a ciki ki soya idan ya kusa gama soyuwa sai kisa grated kayan miyan ki a ciki ki soya su tare
- 3
Idan ya soyu sai kisa ruwan tafashen naman sai ki kara ruwa daidai yanda zai dafa miki su sai kisa maggi da curry ki barshi ya tafaso idan ya tafaso sai ki sa macaroni ki bashi ya dafu kaman na biyu zuwa uku haka Sai ki zuba taliyan daya tafaso sai ki juye green beans din carrot din ki juya Sai ki rufe ki barshi ya nuna idan ruwan ya kusan tsotsewa Sai ki kashe shikenan
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11944670




sharhai (2)