Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki hade semo dinki d flour waje daya sai kijuya su kisa salt d sugar kadan kisake juyawa sai kisa yeast kisake juyawa sai kisa ruwan dumi kikwaba sosai sai kasa Leda abakin robar kisashi agu mai dimi yatashi
- 2
Bayan kamar 2hr sai ki dauko kullin kiss masa kwai2 kisa ludayi kijuya sosai sai kidauko ruwa kikara akan kullin yadaiyi yanda kike so kaurin, sai kisa baking powder kisake juyawa.
- 3
Sai ki Dora kaskon wainar kisa mai yayi zafi sai kifara soyawa, haka zakiyi harkigama, shi amfanin sa flour a wainar semo tana hanashi yayi wannan tuwan d yakeyi inkinsa flour kuma zakiga cikinsa baiyi tuwo tuwannanba
- 4
Inkingama sai kisa a kwano ko flacks kibarta tadansha iska kafin kirufeta, zaki iyacinta d duk wani nau in miyar d kikeso aci dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes









sharhai