Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samu baban kwano ki zuba awarar ki sai ki murmusa ta sosai ko ina ya fashe
- 2
Sai ki samu tarrugunki da albasa ki wanke sai ki bare taffarnuwan ki kiyi grating
- 3
Sai ki zuba a cikin awaran ki sai ki kawo maggi ki barbada sai ki kawo kwanki ki fasa guda 10 a ciki sai ki juya sosai ko ina ya hade ki kawo curryn ki ki zuba
- 4
Sai ki samu bakan Leda ki kukula shi sai ki samu tukunya sai ki sa ruwa kisa awaran ki ki barta har ta dahu sosai
- 5
Sai ki samu kwano ki fasa kwai ki guda 3 ki kada ki sa maggi da curry ki yanka albasa ki
- 6
Sai ki samu awaran ki ki cire a Leda ki barta ta dan huce sai ki yayanka sai ki samu mai ki zuba a frying pan in yayi zafi sai ki sa awaranki a kwai sai ki zuba ki soya in ta soyu sai ki kwashe
- 7
Shikenan a zuba aci da sauce aci dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes









sharhai