Dambun shinkafa

Umman Amir And Minaal 🎂🍜🍝 @aishamijina
Dambun shinkafa
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki barza shinkafa, saiki wanke tsakin ki aje, ki gyara zogala ki wanke itama, ki jajjaga tattasai da tarugu.
- 2
Zaki hada shinkafar da zogala kiyi mixing sosai, saikisa ruwa a pot, ki Dora a wuta ki dora kwando (kwalanda) a Kai, saiki nemi buhu ki yanka, ki wankeshi, saiki shinfidashi a cikin kwandon
- 3
Ki kawo hadin tsakin shinkafa da zogala ki zuba, saiki barshi ya turara kamar minti 15 saiki sauke ki juye a roba mai dan girma
- 4
Saiki sa tarugu, tattasai, albasa, mangyada, curry, kayan kamshi kiyi mixing sosai komai ya hade, saiki kara mayar dashi a cikin kwandon ya kara turara kamarna minti 10 saiki sauke shikenan... Aci da zafi..
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12805696



sharhai