Umarnin dafa abinci
- 1
Za'a gyara waken soya a cire duk datti da tsakuwa a wanke shi sai a markada shi yayi laushi.
- 2
Daga an markada sai a zuba manja cokali daya shi zai hana kumfar waken, a tace da abin tata sai a dora a wuta.
- 3
Idan ya kusa tafasa sai a bude tukunya don kar ya zuba, idan ya tafasa sai a zuba ruwan tsami ya cigaba da dahuwa, a hankali za'a ga yana hadewa.
- 4
Za'a grating attaruhu da albasa sai a zuba awarar ta hade tare da shi.
- 5
Idan ta gama hadewa sai a kawo abin tata a kwashe a cike a bar shi ya tsane, idan ta huce sai a yanyanka.
- 6
Idan ana kwashe za'a iya barbada gishiri a ciki ko kuma kafin a soya bayan an yanka a zuba a cikin ruwan gishiri.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/13373941




sharhai