Tsire

Sakamakon Sallah laya da akayi a kwai nama kuma anaso a sarafa nama izuwa nauika kalla kalla wannan yasa na sarafa nama nayi tsire kuma yayi dadi sosai sosai
Yan gidan mu nata santi
#Sallahmeatcontest
Tsire
Sakamakon Sallah laya da akayi a kwai nama kuma anaso a sarafa nama izuwa nauika kalla kalla wannan yasa na sarafa nama nayi tsire kuma yayi dadi sosai sosai
Yan gidan mu nata santi
#Sallahmeatcontest
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samu naman ki tsoka zallah sai ki yanka shi falefale
- 2
Sai ki kawo yajinki da maggi ki zuba ki guya sai ki kawo tarugu da tafarnuwa ki yi grating
- 3
Sai ki zuba sai ki samu citta ki zuba sai ki kawo albasa ki yayanka kanana ki zuba
- 4
Sai ki samu Leda ki juye ki sa a fridge na tsawon hour daya sai ki Ciro shi
- 5
Sai ki samu frying pan ki zuba sai ki kawo ruwa kaman cokali 5 ki zuba sai ki rufe ki barshi ya Dan dahu har ruwan ya gafe abunda yasa ake dafashi saboda in kazo kasawa in ka gama tsiren ka yayi laushi
- 6
Sai ki kawo kwanon ki ki barshi ya sha iska sai ki samu kuli kuli ki ki shafa shi a kan namanki ko ina yaji
- 7
Gashi nan
- 8
Sai ki samu man gyada ki zuba akai kadan kadan yanda kulin ki zai kama jikinshi. Sai ki kawo tsinken tsire sai ki jera ki ki kara zuba mai kadan
- 9
Sai ki samu garwashi ki daura raga raga na oven sai ki jera tsiren ki kinayi kina juyawa kina kara mai kadan harya gasu shikenan
- 10
Aci dadi lafiya
- 11
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
















sharhai