Farfesun Naman rago

Walies Cuisine @ummuwalie
Wannan na Aunty Jamila na ita kadai gaskia, data jawoni Hausa app kuma na hwara jin Dadi nai walle. Amma dai yayi Dadi yayi yaji yaji. Baa cewa komi kam
Farfesun Naman rago
Wannan na Aunty Jamila na ita kadai gaskia, data jawoni Hausa app kuma na hwara jin Dadi nai walle. Amma dai yayi Dadi yayi yaji yaji. Baa cewa komi kam
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki daddatsa qashin tare da tsokàr sai ki yanka madaidaita ki dauraye naman da ruwa sai ki zuba a tukunya mai tsafta.
- 2
Sai ki zuba jajjagen tarugu da albasa ki zuba tafarnuwa da citta kisa gishiri, mai, kayan yaji da dandano sai ki zuba ruwa ki ruhe tukunyar ki aza a saman wuta.
- 3
Bayan ya dau lokaci saman wuta sai ki duba idan yayi laushi kuma qamshi zai bi har makwabta, sai ki sauke sai ci.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15343471

sharhai (13)