Soyayyar shinkafa
Barka da juma'a
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na jika shinkafata tsawon minti 30 zuwa 40 kafin na dora tukunya na zuba ruwa da curry na wanke shinkafar na zuba
- 2
Da shinkafata ta tafasa se na tsane ta a kwando
- 3
Dama can na tafasa anta na yanka ta kanana
- 4
Se na dora tukunya a wuta na zuba mai da albasa da anta da jajjagen tarugu kadan da karas da koren wake na soya su sama-sama
- 5
Na zuba kayan kamshin da nayi amfani dasu na zuba shinkafar a ciki ina juyawa na zuba kayan dandano
- 6
Haka nayi ta juya ta har tsawon minti goma zuwa sha biyar se na kashe wuta na yanka albasa akai na rufe ya turara
- 7
An gama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15677072










sharhai (6)