Soyayyen cuscus da miyan kabeji

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yanada dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Cuscus
  2. Attarugu
  3. Karas
  4. Koren tattase da koren wake
  5. Kabeji
  6. Albasa
  7. Mai
  8. Maggi dasauran kayan dandano da kikeso
  9. Kifi soyayye
  10. tafarnuwaCitta da

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki wanke su kabejinki ki yayyankasu sai kinajiye agefe sannan kiyanka albasa itama kibajiye agefe sai ki jajjaga attaru da tafarnuwa da citta duka ki ajiye agefe

  2. 2

    Sannan kidaura tukunya a wuta kisa mai sannan kisa albasa idan albasa yakusan soyuwa sai kisa citta da tafarnuwa da kika jajjaga bayan yasoyu sai kizuba jajjagen attarugu sannan kizuba cuscus kidan soya sai kisa su Maggi da curry da thyme sannan kisa kurkur da sauran sinadaran

  3. 3

    Sai kiyi tasoyawa zuwa minti biyar sannan kisa ruwa daidan yanda zai dafamiki cuscus din sannan kisa su karas dinki da kabeji dazauran kayakin kijujjuya komai yahade sannan kirage wuta kibarshi yadahu shikenan sai kisauke

  4. 4

    Miya......zaki daura tukunya a wuta kisa Mai kadan sannan kisa albasa yadan soyu sai kisa citta da tafarnuwa sannan kizuba jajjagen tumatur da attarugu sannan kisa Maggi curry thyme da sauran sinadar dandano na girki sai kidan soyata sama sama sannan kizuba soyayyen kifinki saikuma kisa karas da kabeji sai kibarshi yadahu sai kisauke shikenan angama

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes