Gwaben kamzo zogale da kayan lambu

Mrs Mubarak @maanees_kitchen
#GARGAJIYA Na hada wannan girkin ne anatayin kwalama domin ya kasance abincin rabarmu kuma ya kayatar da iyali na sunji matukar dadinshi.
Gwaben kamzo zogale da kayan lambu
#GARGAJIYA Na hada wannan girkin ne anatayin kwalama domin ya kasance abincin rabarmu kuma ya kayatar da iyali na sunji matukar dadinshi.
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na daka kamzo na rege shi nasa ruwan dumi na barshi ya jika
- 2
Sannan na wanke latas na yanke nakuma kara wankewa daga baya
- 3
Na daka kuli da tanka da kuma magi dai dai bukata
- 4
Na wanke tumatir tarugu da albasa sannan kuma na yanka su
- 5
Na kara wanke zogale itama na aje a gefe
- 6
Daga karshe na matse kazo na na zuba latas,kayan tumatir da kuma zogale da kuli na kara barbada magi star na har mutse muka cenye
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16013517




sharhai (2)