Kayan aiki

minti 30mintuna
3 yawan abinchi
  1. Gero gwangwani 2
  2. Manja me kyau soyayye
  3. Yajin borkono me dadi
  4. Maggi
  5. Kabeji da latas da albasa da tumatir
  6. Gishiri dan dai dai

Umarnin dafa abinci

minti 30mintuna
  1. 1

    Zaki surfa gero ki baza shi ya dan sha iska sai ki murtsike shi ki bushe dusar sai ki wanke ki rege shi saboda zaa iya samun tsakuwa a ciki

  2. 2

    Ki dora tukunya a wuta ki zuba ruwa in ya tafasa ki dauko geronki da kika wanke ki zuba a ciki ki dafa shi kamar dahuwar shinkafa yayi wasar wasar

  3. 3

    Ki dauko kabeji da latas da tumatir da albasa ki yanka su kananu sai ki zuba ruwa akai ki saka gishiri ki barshi na yan mintuna sai ki tsane shi ki kara dauraywa

  4. 4

    In geronki ya dahu sai ki sauke ki zuba a faranti ki dauko yajinki me dadi ki barbada akai in kina so zaki iya kara maggi sai ki zuba manja ki dauko ganyen ki ki hada dashi aci dadi lapiya

  5. 5

    Zaki iya yi da wake kamar yadda ake shinkafa da wake zan kawo shi a gaba amma wannan na gero ne zallah

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hafsatmudi
Hafsatmudi @Hafsatmah08
rannar
Bauchi

sharhai (4)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Kuna ta cin dadinku baa gayyace mu ba 😩

Similar Recipes