Tuwon shinkafa miyan Ganyen Alayyahu Da Kayan Cikin Rago

Jamila Hassan Hazo
Jamila Hassan Hazo @Jermeelerh2

Mahaifiyata masoyiyar wannan girkine gareta naga wannan samfurin.
#gargajiya

Tuwon shinkafa miyan Ganyen Alayyahu Da Kayan Cikin Rago

Mahaifiyata masoyiyar wannan girkine gareta naga wannan samfurin.
#gargajiya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1hr 20mns
uku
  1. Shinkafan tuwo/farar shinkafa gwangwani biyu da rabi
  2. Mangyada gwangwani daya da rabi
  3. Tattasai manya guda shida
  4. Attarugu guda hudu
  5. Albasa manya biyu
  6. Citta yatsa uku
  7. Kanumfari guda biyar
  8. Kayan cikin rago daidai Ra'ayi
  9. 4 Tafarnuwamanya
  10. Maggi biyar
  11. cokaliGishiri kwatan
  12. Masoro kadan
  13. gwangwaniGyada dakakkiya Rabin
  14. Ganyen Alayyahu da ganyen albasa ayanka qananu awanke fess

Umarnin dafa abinci

1hr 20mns
  1. 1

    Tuwon za'a fara da zuba ruwa madaidaici atukunya akan wuta ya tafasa

  2. 2

    Sai awanke farar shinkafarki tass akawo azuba akuma rufe abarshi yadahu bisa madaidaicin wuta

  3. 3

    Akawo muciya atuqeshi tass sai azuba mangyada kamar rabin madaidaicin ludayin miya akai acigaba da tuqawa

  4. 4

    Rufe tuwon da murfi yasulala sai kwashewa.

  5. 5

    Miyar kuma:
    Wanke kayan cikin rago tsaff, juye atukunya, zuba tafarnuwa dakakke sa citta da Kanumfari da masoro da maggibiyu da gishiri kadan shima,daura Akan wuta arufe yadahu ahankali ligif sai asauqe a ajiyeshi agefe

  6. 6

    Daura wata tukunya daban akan wuta,zuba mai inyafara zafi zuba yankakken albasa da tafarnuwa da tattasai da attarugu jajjagegge sai ayita soyawa ana juyawa da ludayin miya

  7. 7

    Akawo dafaffiyar kayan cikin ragonnan dake gefe azuba asoya tare na minti biyar sai azuba ruwan da aka dafa kayan cikin ragon akai akuma zuba dakakkiyar gyada sai yadahu na minti ukku sai akawo Alayyahu da ganyen albasa ajuye aciki agauraya arufe minti daya sai asauqe

  8. 8

    Aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Jamila Hassan Hazo
rannar
I Drive Pleasure While Cooking
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes