Alala Mai miya
Umarnin dafa abinci
- 1
Farko zaa samu wake a surfa Shi a wanke sosai a cire mashi hanci har sai dusan ya fita duka
- 2
Sai a kawo tattasai tarugu albasa da aka gyara aka wanke a zuba a cikin waken da aka wanke sai a niqa yayi laushi sosai
- 3
Bayan ya niqu sai a kawo magi da dakakkar tafarnuwa, spices,albasa,a zuba ciki a juya har sai sun hade jiki sosai
- 4
A buga Shi sosai sosai sai a zuba mangyada ko manja duk Wanda Ake buqata,a cigaba da juyawa ana buga Shi idan ya bugu sai a qara ruwa Kada yayi ruwa sosai
- 5
Sai a kawo daffafen kwai da aka yanka da soyayyen kifi a zuba ciki a dauko alayyahu da aka yanka Shi aka wanke a zuba shima a juya sai a kulla a Leda ko a zuba a container a juye gefe
- 6
Sai a daura ruwa a wuta yayi zafi sosai sai a dauko kulallen alala a saka a cikin ruwan a rufe tukunya a barshi tsawon minti 40 sai a sauke.
- 7
A jajjaga tarugu da albasa a ajiye gefe,a yanka albasa size da shape da Ake buqata a ajiye gefe
- 8
A zuba mangyada a frying pan idan yayi zafi sai a zuba jajjagen tarugu da albasa a saka spices da seasoning a juya idan ya Fara soyuwa sai a zuba albasa a rufe kaman minti 4-5 sai sauke...aci dadi lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (2)