Semolina Balls
Umarnin dafa abinci
- 1
A debi garin semolina Kofi biyu, sai a niqa shi a blender, za aga yayi laushi sosai Kamar flour,a zuba a roba, a nemi yeast karamar cokali daya a zuba.
- 2
A zuba gishiri qaramar cokali daya, a gauraye a debi ruwan dumi a kwaba dashi kamar panke.
- 3
A rufe hadin a barshi a wuri me dumi ya samu kamar minti 30-40. Bayan ya tashi sai a nemo dakakken nama wadda ta sulala, ko Kuma kifi idan ana buqata,sai kayan dandano,atarugu da albasa.
- 4
A yanka albasa kanana, a jajjaga atarugu a fasa Maggi idan ana buqatar wasu kayan dandanon ana iya karawa a ciki. Sai a juye a cikin kwabin semolinar a gaurayesu sosai da sosai su hade.
- 5
Bayan an kwaba dakyau sun hade sai a daura Mai a wuta tayi zafi, a rinqa debar hadin Nan Ana jefawa cikin Mai. A soya ta Kamar panke a wuta Mara karfi sosai.
- 6
Bayan an soya an kwashe ta a mazubi, za a iya cinta da romon mama ko kifi, shayi ko juice ko a cita haka. Tana da Dadi sosai.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





















sharhai (2)