Yar bagalaje (wainar rogo/ kosan rogo)

Khady Dharuna @antynanah2022
Abincin karin kumallo me sauki. (Breakfast) Kusan kowa yana sonta. Tana da dadi sosai. D ftn za ku gwada don jin dadin ku.😂😀😃
Yar bagalaje (wainar rogo/ kosan rogo)
Abincin karin kumallo me sauki. (Breakfast) Kusan kowa yana sonta. Tana da dadi sosai. D ftn za ku gwada don jin dadin ku.😂😀😃
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a zuba garin a roba a ciccire dattin da tsakuwar.
- 2
Sai a kawo ruwan zafi a zuba akai har ya sha kan garin. A rufe yayi kamar mintuna 5.
- 3
A zuba kayan hadin gaba daya a juya ya hade jikinsa
- 4
Sai a dunga mulmulawa
- 5
Sannan a fadada da hannu
- 6
Sai a soya a cikin ruwan mai me zafi. Note: idan mai beyi zafi ba zata sha miki mai.
- 7
A bari ta yi ruwan zuma shine ta soyu sai a juya a kwashe
- 8
A ci da zafinta. Ni dai da kunun tsamiya nayi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16384158









sharhai (4)