Faten doya da wake

sassy retreats @sadiya6694997
#WAKE doya da wake a wannan season din yana da dadi sosai a wannan yanayin
Faten doya da wake
#WAKE doya da wake a wannan season din yana da dadi sosai a wannan yanayin
Umarnin dafa abinci
- 1
Yar uwa da farko zaki dafa waken ki ya dahu sosai yayi laushi sai ki ajje a gefe ki dauko doya itama ki fere ta ki ajje
- 2
Sai ki samu tukunya ki zuba jajjagen ki da tumaturin leda ki soya su soyu sosai sai ki zuba ruwa kadan bada yawa ba daidai Wanda zai dafa miki doyar ki
- 3
Bayan nan sai ki saka spices dinki in ya ta fasa ki zuba doya din ki saka kifin ki ki rufe in ya kusa Dahuwa sai ki dauko waken nan da kika dafa ki zuba akai ki saka yankar kiyar albasa ki rufe har sai doyar ki tayi laushi sosai
Abincin ku ya kammala ❤️
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16642780







sharhai (2)