Tuwon shinkafa miyar wake

#omn Ida shinkafan tuwa ragowan Wanda nayi waina ne shine nace bari nayi da waken danake dashi,kuma haka nayi miyata babu nama babu kifi kuma yayi dadi sosai 😋😋😋
Tuwon shinkafa miyar wake
#omn Ida shinkafan tuwa ragowan Wanda nayi waina ne shine nace bari nayi da waken danake dashi,kuma haka nayi miyata babu nama babu kifi kuma yayi dadi sosai 😋😋😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki jika shinkafan tuwan na Dan wani lokaci kafin ki fara girkin ki, sannan ki daura tukunyarki
- 2
Da ruwa ya tafasa sai ki zuba shinkafan ki ya nuna sosai yada zai tuku yayi kyau sai ki malmala ko kuma ki zuba a Leda ki daure
- 3
Sai ki zuba manja acikin tukunyarki sai kisa albasa da garlic and ginger sannan ki zuba kayan miyarki da kika gyara ki soyasu
- 4
Zaki gyara kayan miyarki kiyi blanding ko kuma ki jajjagasu
- 5
Sai ki zuba ruwa ki daurashi akan wuta ya nuna Zaki Dan jefa kanwa kadan saboda ya nuna sosai
- 6
Idan ya nuna sai ki dauko wannan kayan miyarki da kika soya sai ki zuba
- 7
Akai ki juya ya hade sosai sai ki saka ludayi ki Kara farfasa waken yadda zai narke sosai idan kika ga yanuna zakijishi Yana kamshi
- 8
Sai ki dauke albasa ki yankashi kanana ki zuba yayi Kamar 5min sai ki sauke
- 9
Sannan dama kin wanke waken ki kin cire bayun Kamar yadda zakiyi alala haka Zaki wanke shi,
- 10
Keywords
Similar Recipes
More Recipes









sharhai