Miyar waken suya

Ita wannan miyar zaka iya cinta da tuwo waina sinasir funkaso da dai sauransu Akwai dadi sosai
Miyar waken suya
Ita wannan miyar zaka iya cinta da tuwo waina sinasir funkaso da dai sauransu Akwai dadi sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na gwara waken suyana saina wamke Kayan miya na hada aciki na markada na ajje agefe
- 2
Sannan nawanke nama saina dora tukunyata awuta nasa nama albasa da Kayan kanshi da dan gishiri nabarshi ya silala sannan na sauke najuya saina maida tukunyar wuta nasa manja dayayi zafi na juye Kayan miyana da waken suya Wanda na nika nabarshi yadahu sosai saboda gafin waken suyar yafita sbd inba abari yafitaba miyar zata dinga gafi kuma bazatayi dadiba.
- 3
Bayan na tabbatar gafin waken ya fita saina juye namannan ciki da gandar da kuma bushashshen kifin nan na barsu suka dahu suma.
- 4
Sannan nasa alaiyahu,dandano,kori kayan kanshi suma nabasu yan mintina nasauke shikenan saici.
- 5
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
















sharhai (2)