Dafadukan taliya da kayan lambu

Dafadukan taliya da kayan lambu
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki jajjaga kayan Miya ki Dora tukunya kisa Mai kiyanka albasa kibari ta soyu
- 2
Saiki zuba jajjagen kisoya sama sama saikiyi sanwa kibari su tafasa
- 3
Ki wanke wake kizuba kibari ya dahu na 10mnt saiki sa taliya
- 4
Idan kikaga sun dauko dahuwa saiki sa curry,maggi da gishiri ki rufe sai ruwan sunyi yadda kikeso saiki zuba su carrot naki ki kashe wutar zafin abinci zai dafa su
- 5
Note;
Ni bana saka maggi a jollop sai ta dahu ruwan sunkusa tsotsewa sbd idan kikasa maggi Kuma girkin ki na Neman Karin ruwa toh abincin ki salabcewa zaiyi - 6
Haka carrot saina gama girki nakeso nasa shi sbd banason inacin carrot a girki ya dafe balanta cucumber da cabbage duka suma tiriri na girki na dafa Maka su
- 7
Idan kina bukatar carrot yadahu saiki sa a dahuwar ki basai kinzo karshe ba
- 8
Ngd
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai