Soyayyar miyar jajjage

Salwise's Kitchen @cook_16516066
Soyayyar miyar jajjage
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za'a gyara kayan miyar,a bud'e ciki a wanke tas!
- 2
Sai, a kwashe a sanya tukunya,a d'ora a wuta, a barshi ya nuna har ruwan ya k'afe.
- 3
Sai a tafasa Nama,da Maggi da albasa
- 4
Sannan a d'ora watar "yar tukunyar,a zuba Mangyada a soya da albasa sama-sama
- 5
Sannan azuba, wannan kayan miyar da aka tafasa.
- 6
Sai a zuba Maggi, gishiri,citta da Kanunfari,sannan a zuba namar
- 7
Ayi ta soyawa, na kamar mitoci ashirin,sannan a sauke
- 8
Sai a jajjaga a turmi ko Gireta ko a bilenda
- 9
Za'a iya Ci da Farar shinkafa, ko Teba ko soyayyar doya. Aci lafiya
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/8273036



sharhai