Yoghurt
Yanada sauqi da dadi sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki zuba madarar ki ta gari a cikin robar da zaki hada yoghurt din
- 2
Sai ki zuba mata ruwa Wanda basuda zafi ki juya sosai har ta hadu da kyau
- 3
Sai ki dauko tafasashen ruwan zafin ki ki sake zubawa a cikin hadin madarar
- 4
Ki saka flavor
- 5
Ki saka sugar
- 6
Ki saka Culture kadan,in bakida culture sai ki nemi yoghurt Wanda a ingredients din shi akwai (DVS culture)a ciki,sai ki saka kofin awo guda na yoghurt din a ciki
- 7
Ki juya hadin gaba daya kamar haka
- 8
Ki rufe hadin da marufi ki boyeshi a wuri me dumi har tsawon awa goma (10hrs)
- 9
Idan lokacin yayi zakiga yoghurt din ki ya koma haka,zi kuma Baku kamshin yoghurt
- 10
A kula! Idan akayi hadin bayaso ana yawaita budashi,idan son samu ne idan kika rufe shi kada ki buda shi sai bayan awa 10
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai